Shin ganyen darbejiya yana maganin Corona Virus ? – alwilayah tv hausa

alwilayah tv hausa

Today: Thursday 01 December 2022

اِلهى‏ عَظُمَ الْبَلاءُ، وَ بَرِحَ الْخَفآءُ، وَانْکشَفَ الْغِطآءُ، وَانْقَطَعَ الرَّجآءُ، وَ ضاقَتِ الْأَرْضُ وَ مُنِعَتِ السَّمآءُ، و اَنْتَ الْمُسْتَعانُ وَ اِلَيک‏ الْمُشْتَکى‏، وَ عَلَيک الْمُعَوَّلُ فِى الشِّدَّةِ وَالرَّخآءِ، اَللّهُمَّ صَلِّ عَلى‏ مُحَمَّدٍ وَ الِ مُحَمَّدٍ، اُولِى الْأَمْرِ الَّذينَ فَرَضْتَ عَلَينا طاعَتَهُمْ، وَ عَرَّفْتَنا بِذلِک مَنْزِلَتَهُمْ، فَفَرِّجْ عَنا بِحَقِّهِمْ، فَرَجاً عاجِلاً قَريباً کلَمْحِ‏ الْبَصَرِ اَوْ هُوَ اَقْرَبُ، يا مُحَمَّدُ يا عَلِىُّ، يا عَلِىُّ يا مُحَمَّدُ، اِکفِيانى‏ فَاِنَّکما کافِيانِ، وَانْصُرانى‏ فَاِنَّکما ناصِرانِ، يا مَوْلانا يا صاحِبَ‏ الزَّمانِ، الْغَوْثَ الْغَوْثَ الْغَوْثَ، اَدْرِکنى‏ اَدْرِکنى‏ اَدْرِکنى‏، السَّاعَةَ السَّاعَةَ السَّاعَةَ، الْعَجَلَ الْعَجَلَ الْعَجَلَ، يا اَرْحَمَ الرَّاحِمينَ، بِحَقِّ مُحَمَّدٍ وَ آلِهِ الطَّاهِرينَ.

Social Network

Shin ganyen darbejiya yana maganin Corona Virus ?

Tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi magana a kan kwayar magani ta chloroquine wajen magance matsalar cutar Corona, mutane da dama sun karkata zuwa ga amfani da wannan magani, amma a Nigeriya ….

Amma a Nigeriya mutane suna ta kokarin yin amfani da ganyen darbejiya domin kare kai daga wannan cuta.

wannan lamari ya tayarwa da masana harkar lafiya hankali, Prof Hadiza Nuhu tsohuwar malamar jami’a, kuma Babbar mai bincike daga tsangayar bincike akan itatuwa ta yi bayanin yadda wannan al’amari ya tayar mata da hankali, ta bayyana cewa akwai bambanci tsakanin kwayar magani ta chloroquine da ganyen darbejiya, sannan ta kara da cewa wannan magani ba a samar da shi gada wannan ganye ba, duk da cewa shima ganyen ana iya yin amfani da shi wajen magance cutar maleriya amma fa shi ba chloroquine ba ne.

Malamar ta yi bayani a kan hadarin da ke tattare da shan wannan ganye ba bisa ka’ida ba, domin yin hakan yana da matsalolin da kan iya haifar da wasu cututtuka a jikin mutum, saboda haka bai dace a rika daukar ganyen ba ana zubawa a abinci ko a bin sha ba.

Yadda a ke amfani da ganyen shi ne kamar haka: ana samun wannan ganye kwaya bakwai sai a wanke shi, sai a tafasa shi a ruwa lita daya sai a sha shi a tsawon awa 24, kuma kada a sha wannan magani fiye da kwana 3 , shima kwana ukun ba a jere ba, wato in an sha yau to kada a sha gobe sai jibi sai a sake tsallake kwana daya sai a sha, wannan zai yi wa mutum maganin zazzabin maleriya har tsawon wasu watanni, ya danganta da inda mutum yake rayuwa da kuma yadda sauro ya ke a wannan guri.

Hattara! duk wanda yasan yana ciwon hanta ko ciwon kunne na rashin-ji ko mai yawan rashin lafiya to bai kamata ya sha wannan magani ba, ta kara da cewa mace mai ciki ma kada ta sha. Su kuma yara ana ba su rabin na babban mutum ne.

Daga karshe ta yi kira da a dogara ga Allah da kuma dagewa wagewa wajen Addu’a.

Alwilayah TV Hausa

(Visited 433 times, 1 visits today)

Comment (4)

  1. Babu ƙamshin gaskiya a maganar cewa iccen darbejiya/dalbejiya/bedi/neem/dogon-yaro yana da tasiri wajen baiwa mutum kariya daga kamuwa ko warkewa daga cutar corona virus. Hukumar World Health Organization ta yi musun cewa tafarnuwa, ko lemun tsami ko kwankwadar ruwa na maganin corona virus (https://www.cnbc.com/amp/2020/02/04/who-pushes-back-on-coronavirus-misinformation-and-bogus-cure-claims.html). Hukumar ta jaddada cewa corona ba ta da maganin da ya wuce matakan kariya ta hanyar wake hannu da sabulu, nisantar mai ciwon corona da sauransu (https://www.who.int/emergencies/diseases/novel-coronavirus-2019). Zancen cewa neem nada tasiri akan corona virus ya fito daga ƙasar India, ta hanyar ilimin magungunan gargajiya na Ayurveda/Unani medicine/homoeopathy (https://pib.gov.in/pressreleasepage.aspx?prid=1600895). Ilimin magungunan gargajiya na Ayurveda ilimine iyaye da kakanni, wanda bai dogara da ilimi na kimiyya da fasaha ba, kamar yadda magungunan gargajiya na bahause basu dogara akan bincike/binkice na kimiyya da fasaha na zamani ba. Abun sai a hankali, hasashe ne kawai.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *