BAYANAN WAYAR DA KAI AKAN CUTUKA MASU YADUWA – alwilayah tv hausa

alwilayah tv hausa

Today: Thursday 01 December 2022

اِلهى‏ عَظُمَ الْبَلاءُ، وَ بَرِحَ الْخَفآءُ، وَانْکشَفَ الْغِطآءُ، وَانْقَطَعَ الرَّجآءُ، وَ ضاقَتِ الْأَرْضُ وَ مُنِعَتِ السَّمآءُ، و اَنْتَ الْمُسْتَعانُ وَ اِلَيک‏ الْمُشْتَکى‏، وَ عَلَيک الْمُعَوَّلُ فِى الشِّدَّةِ وَالرَّخآءِ، اَللّهُمَّ صَلِّ عَلى‏ مُحَمَّدٍ وَ الِ مُحَمَّدٍ، اُولِى الْأَمْرِ الَّذينَ فَرَضْتَ عَلَينا طاعَتَهُمْ، وَ عَرَّفْتَنا بِذلِک مَنْزِلَتَهُمْ، فَفَرِّجْ عَنا بِحَقِّهِمْ، فَرَجاً عاجِلاً قَريباً کلَمْحِ‏ الْبَصَرِ اَوْ هُوَ اَقْرَبُ، يا مُحَمَّدُ يا عَلِىُّ، يا عَلِىُّ يا مُحَمَّدُ، اِکفِيانى‏ فَاِنَّکما کافِيانِ، وَانْصُرانى‏ فَاِنَّکما ناصِرانِ، يا مَوْلانا يا صاحِبَ‏ الزَّمانِ، الْغَوْثَ الْغَوْثَ الْغَوْثَ، اَدْرِکنى‏ اَدْرِکنى‏ اَدْرِکنى‏، السَّاعَةَ السَّاعَةَ السَّاعَةَ، الْعَجَلَ الْعَجَلَ الْعَجَلَ، يا اَرْحَمَ الرَّاحِمينَ، بِحَقِّ مُحَمَّدٍ وَ آلِهِ الطَّاهِرينَ.

Social Network

BAYANAN WAYAR DA KAI AKAN CUTUKA MASU YADUWA

DAGA DANDALIN KULA DA LAFIYA (I S M A) ISMA@2019-nCoV

MATAKAN KARIYA DA RIGA – KAFIN
CUTAR CORONA VIRUS (COVID-19)🌹[2019-nCoV] 🌹

Courtesy: ISMA MEDICAL CARE INITIATIVES (( Registered Humanitarian & Medical NGO #RC008247 ))
Contact: ismamedicalcareinitiatives@gmail.com GSM 0803 964 9234 // 0706 438 7059 // 0806 261 9356🌹
ISMA@2019-nCoV

Darasi: MATAKAN KARIYA DA RIGA – KAFIN
CUTAR CORONA VIRUS (COVID-19)

ISMA@2019-nCoV

Cutar Corona cuta ce mai saurin yaduwa a tsakanin mutane sakamakon haduwa da kwayoyin cutar masu taurin rai da saurin yaduwa a tsakanin mutane,

Kwayoyin cutar dangin Virus na haddasa cutuka da dama masu kama makoshi da hanyar shakar numfashi.🍇

🌼TABBACIN BULLAR WANNAN CUTA

Lalle akwai inganci ga bayanan cewa annobar wannan cuta ta barke a sassa da dama na duniya kuma lalle cutar na ci gaba da yaduwa kamar wutar daji, za ta iya riskar wuraren da ba ta je ba, don haka a kiyaye, daukar matakan kariya da riga-kafi da addu’o’i ne kawai mafita.🍓

🌻ALAMOMIN CUTAR COVID-19

Zazzabi, Masassara, Jante, watau zafin jiki zai karu sosai ga wanda ke dauke da kwayoyin wannan cuta

Yawan tari, atishawa, mura, yawan kakin majina,

Wahalar shakar numfashi da zafin kirji, kamar masu cutar Asama,

Radadi a makoshi yayin hadiyar wani abu,

Nauyin jiki baki daya da kasala,

Yayin tsanantar ciwon saboda rashin kular gaugawa, alamomin za su iya wuce haka zuwa tabarbarewar kowane sashe da bangaren jiki abinda zai iya sanadin mutuwa idan ba’a tarbi alamomin da gaugawa ba.🍅

🌾YANDA CUTAR KE YADUWA:

Cutar na yaduwa cikin gaugawa ta hanyar haduwa da kwayoyin cutar da wanda ya kamu zai rika fitarwa daga jikinsa, ta hanyar digon yawu ko majina yayin kaki ko atishawa ko tari ko ta hanyar digar miyau yayin magana, 🍉

🌺ZAMAN CUTAR A JIKI

Watau cutar kan shiga jiki ta nuna a jiki ta fara illa ga wanda ya kamu har ya iya yada ta ga sauran mutane idan ta zauna a jiki tsawon kwanaki daga 2 zuwa kwana 14, daga nan duk illolin cutar za su bayyana,🥥

🥀RIGA-KAFIN CUTAR:

Zuwa yanzu babu sinadarin allura ko maganin Riga-Kafin wannan cuta, sai dai daukar matakan kariya da zamu ambata.😇

🍁MATAKAN KARIYA DA RIGA-KAFI🍊

Babbar hanyar kubuta daga wannan cuta shine a KIYAYI HADUWA DA KWAYOYIN CUTAR DANGIN VIRUS MASU SAURIN KISA 😷

A kiyaye mu’amullar saduwa da wanda ya kamu da wanda ake zargin zai iya kamuwa ba’a farga ba.

Ana iya mu’amulla da wanda ake ganin ya kamu ko zargin zai iya kamuwa ya yada cutar a yanayin barkewar Annoba a kalla nisan kafa shidda (6 Feet) a tsakanin juna.

Haka ana samun cuta a cikin yawu da majinar da suka fito daga wanda ke dauke da kwayoyin cutar, don haka a kiyaye saduwa da wadannan daga jikin da suka fito daga baki da hancin wanda ya kamu.

Cikin gaugawa za su iya kaiwa ga hanci ko baki ko makoshin wanda lafiyar sa lau kuma ya dauki cutar nan take. 🍓

🍀KARIN MATAKAN KARIYA DA RIGA KAFI
🚑

Yawaita wanke hannuwa 🙌🏾 da sabulu ko ruwa masu tsafta a dauraye a tsane hannuwa, a saba da haka a kuma koyar da yara haka
wannan wanke hannayen ya kasance a koyaushe ka sami kanka a cikin mutane duk bayan yan mintuna a aiwatar da shi gwargwado, musamman irin yanayin da mu ke ciki na yiwuwar barkewar annobar.

Yawaita amfani da ruwan sinadarai masu kashe kwayoyin cuta (Sanitizers) yayin da aka yi mu’amulla da mutane daban-daban, a shafawa dukkan hannaye a rufe su ruf har su tsane,

Haka a kiyayi yawan tabawa da shafar fuska, watau idanu, hanci da baki da hannuwan da babu tabbacin tsaftar su.

A yanayin barkewar annoba, a kiyayi haduwa ta kut da kut maras dalili kuma barkatai da kowane irin mutum.

Da zarar an ji alamun rashin lafiya musamman zafin jiki a yanayin annoba, to a killace kai, a fita daga cikin iyali a garzaya asibiti.

Mai lafiya ya kiyaye haduwa da duk wani maras lafiya, sai yanayin jinya da matakan kariya na masu jinya.🥭

🌿MATAKAN KARIYA DA RIGA-KAFI:

Idan mutum zai yi tari ko atishawa ya rufe bakinsa da hanci,😷 watau abinda ke fita kada a bari ya fita ya bi iska ya tafi wani wuri.😷

Ta hanyar amfani da hankici ko kyalle mai tsafta ko kuma amfani da kyallen rufe fuska (Face Masks)😷

A saba amfani da takardar goge kazanta (Tissue/Toilet Paper) musamman yayin atishawa ko tari, a rika amfani da bayan hannu maimakon tafin hannu wajen tarbar abinda zai fito daga hanci da baki.

A rika wanke hannuwa lokaci zuwa lokaci da ruwa da sabulun wanka, idan babu ruwa da sabulu kusa ayi amfani da sinadarin Sanitizers wanda ya kumshi sinadarin Alcohol 70% masu kisan kwayoyin cuta.

Hankici da takardar goge kazanta (Tissue/Toilet Paper) a jefar da su nesa da jama’a ta yanda ba zasu iya dawowa su cutar da wani ba.☠

🌴KARIN MATAKAN KARIYA DA RIGA KAFI:

A yanayin annoba, ana bukatar amfani da safar kariya ga fuska😷😷😷 (Face-Mask) a koyaushe ga mara lafiya da mai lafiya wanda ke jinya.😷

Mara lafiya ya kula da sanya wannan safa😷 domin ya taimaka kada ya cigaba da yada cutar a cikin masu lafiya, iyalansa da ma’aikatan lafiya da sauransu.

Haka mai lafiya ya kula, ba dole sai ya sanya wannan safa ba😷 face idan yana jinyar mai fama da cutar kuma ba ya iya sanya safar fuskar saboda yanayin rashin lafiya da bukatuwa ga shakar iska, domin ya taimaka kada ya dauki cutar ta cutar da shi ya kuma yada cutar a cikin masu lafiya, iyalansa da ma’aikatan lafiya da sauransu,

Akwai tabbacin cewa wannan safa 😷😷😷(Face-Mask) na hana cutar shiga baki da hanci idan an kiyaye tsaflafiya.🍍

🎄KARIN MATAKAI:

Inganta matakan tsaftar jiki na maras lafiya da masu lafiya.

Inganta matakan tsaftar muhalli, tufafi, kayan ci da sha, tarkacen daki, kayan kwanciya, kayan magewayi da sauransu.

A yi amfani da sinadaran sabulun wanka da wanki, sinadaran Clean, Omo da sauransu,

Gudanar da addu’o’i🙏🏽🕋🙏🏽 daban-daban musamman a gungu da daidaikun jama’a,

A kuma koyar da kananan yara gabatar da irin wadanann addu’o’i 🙏🏽🕋🙏🏽na neman tsari ga gida da iyali da al’umma baki daya, lalle Allah Ta’alah na maganin kowane irin bala’i da annoba.🙏🏽🕋🙏🏽

🎄HADA SINADARAI MASU KISAN KWAYOYIN CUTA:

A debi sinadarin ruwan bleach babban cokali 5 a zuba a ruwa gallon daya, a motsa a cigaba da amfani da su a matsayin abin gogawa ga hannuwa da goge-goge a daukacin kayan amfani kamar wayar salula, sitiyarin mota, hannuwan babur, keke, kujerin daki, gado, gilashin fuska, zobba da sauransu.

KARIN SHAWARWARI

1) 🍏Yin kyakyawan tanadi na daukacin kayan bukatu na gida a yanayin yiwuwar shiga a wasan buya da wannan cuta,

2) 🍎Tanadin safar hannuwa, safar fuska, sinadaran kisan kwayoyin cuta (Sanitizers / Disinfectant)

3)🍐 Kyallaye masu tsafta a matsayin hankici,

4) Takardun share kazanta (Toilet/Tissue paper)

5) 🍊Ruwa masu tsafta a gida,

🥒🌶🥑🥝🌽🥕
ISMA@2019-nCoV


Courtesy: ISMA MEDICAL CARE INITIATIVES (( Registered Humanitarian & Medical NGO #RC008247 ))
Contact: ismamedicalcareinitiatives@gmail.com GSM 0803 964 9234 // 0706 438 7059 // 0806 261 9356

ISMA@2019-nCoV

(Visited 185 times, 1 visits today)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *