
Coronavirus ta shiga fadar shugaban kasa
Bayyanar cutar ta corona a fadar shugaban kasa ya kasance ne bayan an yiwa Abba kyari shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya gwajin cutar kuma an tabbatar da cewa yana dauke da ita.
Kafafen yada labarai na cikin gida sun bayyana faruwar wannan al’amari a ciki fadar shugaban kasa, al’amarin da ya sanya da dama suna tunanin akwai yuwuwar cewa duk na kusa da Abba Kyari sun kamu da wannan cuta, musamman ma wadanda suke mu’amala da shi yau da gobe.
Ana zargin cewa Abba kyari ya kamu da wannan cuta ce a kasar Jamus bayan wata ziyara ta aiki da ya kai a ranar 7 a wannan watan da muke ciki.
Kasancewar Abba Kyari shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa ya sa da dama daga wadanda suka yi mu’amala da shi a wannan fada damuwa, saboda gudun kada ace suma suna da ita.
Ya zuwa yanzu dai ma’aikatar yaki da cutuka masu yaduwa ta bayyana cewa mutane sama da 40 ne suke dauke da wannan cutar ta coronavirus.
Tambayar da mutane da dama suke yi ita ce bayan Abba Kyari su wa ye suke dauke da wannan cuta a wannan fada?
insha allah duk wanda yake da hannun wajan zaluntar yan uwanmu sai ya kamu da wannan cutar.
Slm alwilayah TV Hausa muna muku fatan alkhairi