
KUNGIYAR JAMA’ATU NASRIL ISLAM TA JA HANKALIN AL’UMMA A KAN CORONAVIRUS
Wannan kungiya da take karkashin jagorancin Sarkin Musulmai ta yi kira da jan-hankali ga al’umma a kan su dage da yin azumi da addu’a a kan wannan cuta da ta addabi Duniya.
A cikin sanarawar da Kungiyar ta fitar, ta bayyana cewa jahilci ne Malami Addini ya karyata wannan cuta, kuma hakan na iya dulmiyar da al’umma a kan cutar.
Sanin kowa ne a arewacin Najeriya wasu daga cikin Malaman Addini sun fito fili sun karyata samuwar wannan cuta, kuma sun ce ita wannan cuta makirci ne.
Sakataren wannan Kungiya ta Jama’atu Dr. Khalid Abubakar, ya bayyana cewa bai kamata a rika jin irin wadannan kalamai daga bakin irin wadannan malamai ba.
Ya zuwa yanzu dai wannan ra’ayi na karyata wannan cuta ya na ta yaduwa cikin mutane, to ko mine ne ra’ayin mutane akan irin wadannan malamai ?
(Visited 98 times, 1 visits today)